Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa Mufti Makram Qadri, malami kuma mufti daga Ahlus‑Sunna a Pakistan, ya bayyana a wani taron tunawa da jagoran shahidi Ayatullah al‑Uzma Sayyid Ali Khamenei (Q.S.) da aka gudanar a birnin Karachi na Pakistan cewa: "A yau idan muka ce muna tare da Iran a wannan yaƙi, ba wai kawai muna goyon bayan wata ƙasa ba ne, a’a muna tare ne da imani da Musulunci.
Ya ƙara jaddada cewa babu wani babban bambanci na asali tsakanin Shi’a da Sunna, kuma waɗanda ke ƙoƙarin haddasa rarrabuwar kawuna a gaskiya suna ƙarfafa shirin maƙiyan Musulunci. Saboda haka ya kamata al’ummar Musulmi su haɗu bisa abubuwan da suke da su na bai ɗaya.
Mufti Makram Qadri ya kuma ce: "Jagoran shahidi, Ayatullah al‑Uzma Sayyid Ali Khamenei, ya tarbiyantar da wata al’umma wadda tun da dadewa ta shirya kanta domin fuskantar Amurka. Kasancewar biranen karkashin ƙasa na makamai masu linzami a Iran yana nuna cewa wannan shiri ya fara ne tun shekaru da dama da suka wuce. A yau, ko da yake jagoran ya yi shahada, amma ɗansa, Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamenei, ya ɗauki wannan tutar, kuma shi ne jagoran dukkan al’ummar Musulmi.
Ya sake jaddada cewa: "Idan muka ce muna tare da Iran a wannan yaƙi, ba wai kawai goyon bayan wata ƙasa ba ne, a’a tsayawa ne tare da imani da Musulunci."
Mufti Makram Qadri ya kuma yi ishara da ayyukan masu haddasa rikicin mazhaba a shafukan sada zumunta, inda ya ce wasu mutane masu tsattsauran ra’ayi suna yada farfaganda ta addini a kan Iran domin haifar da sabani. Ya ce irin waɗannan ayyuka a zahiri suna amfanar Amurka da Isra’ila. Idan aka duba da kyau, Shi’a da Sunna ba su da wani bambanci mai mahimmanci, kuma suna iya kasancewa tare.
Ya ƙara cewa Imam Bukhari ya ruwaito hadisai daga wasu masu ruwaya ‘yan Shi’a, wanda hakan ke nuna cewa a wajensa Shi’a ma mutane ne masu imani. Don haka, idan Imam Bukhari yana da wannan fahimta, babu wani matsayi ga maganganun masu haddasa rarrabuwa.
Wannan masani na addini ya kuma yi magana kan ilimin kalam na Ahlus‑Sunna, inda ya ce a cikin Ahlus‑Sunna akwai manyan malamai biyu a wannan fanni: Abu Mansur al‑Maturidi da Abu al‑Hasan al‑Ash’ari. A bangaren aqida, Ahlus‑Sunna ko dai Maturidi ne ko Ash’ari. Wadannan manyan malamai sun bayyana ginshikan imani kamar imani da Allah, ManzonSa, Lahira, mala’iku, da kuma cewa alheri da sharri duk daga Allah suke. Shi’a ma suna yin imani da waɗannan ginshikai gaba ɗaya.
A ƙarshe Mufti Makram Qadri ya jaddada muhimmancin haɗin kai, yana mai cewa: "Lokacin da Allah ya umarci Annabi a cikin Alƙur’ani da ya kira Ahlul‑Kitab zuwa ga kalma ta bai ɗaya, wato tauhidi da nisantar shirka, to me ya sa mu ba za mu haɗu bisa abubuwan da muke da su na bai ɗaya ba duk da bambancin mazhaba?" Ya ce wutar rarrabuwa ana kunna ta ne ta wasu mutane masu son anfani na kansu. A yau wajibi ne mu tsaya tare da Iran, domin hakan a zahiri tsayawa ne tare da imani.
Ra'ayinka